Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Business
  • Education
  • Featured
  • Health
  • Politics
  • Sports
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram
Facebook Instagram TikTok
BROWN PIGEON MEDIA
SUBSCRIBE
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    Members Reps Raise Concern Over Rejection of Corps Members by Government Agencies

    June 5, 2026

    Tinubu Ya Yaba Da Rawar Sojin Ruwa Wajen Kare Arzikin Najeriya

    June 2, 2026

    TINUBU: CIRE TALLAFIN FETUR YA CECI NAJERIYA DAGA DURKUSHEWAR TATTALIN ARZIKI

    May 30, 2026

    GWAMNATIN TARAYYA TA AYYANA RANAKUN HUTUN BABBAR SALLAH A NAJERIYA

    May 26, 2026

    Yan Sanda a ƙasar Turkiyya Sun Gano Baƙin Haure 30 da aka Boye a Cikin Wata Tankar Mai

    June 5, 2026

    Saudiyya Ta Raba Alƙur’ani Miliyan 1.9 Ga Alhazan Bana

    June 2, 2026

    AN HANA YIN LAYYA DA BIJIMIN “DONALD TRUMP” A BANGLADESH

    May 28, 2026

    MAHAJJATA MILIYAN 1.6 SUN HALLARA A FILIN ARAFAT DOMIN SAUKE FARALI A AIKIN HAJJI

    May 26, 2026

    NYA- Kwankwaso’s Alliance and the Question of Northern Political Identity

    June 5, 2026

    OFFICIAL STATEMENT ON THE RELOCATION OF THE NATIONAL AGENCY FOR THE GREAT GREEN WALL HEADQUARTERS TO KANO STATE

    June 5, 2026

    ONE KANO AGENDA HAILS FG OVER RELOCATION OF GREAT GREEN WALL AGENCY HEADQUARTERS TO KANO, URGES STATE TO LEVERAGE OPPORTUNITIES

    June 5, 2026

    Kano Families Return to Charcoal as Cooking Gas Prices Rise

    June 5, 2026
  • Business

    Dangote Industrialising Africa– NCCIMA DG

    May 17, 2026

    INEC TA BUKACI MASU RIJISTAR KATIN ZABE A KANO DA SU JE SU DUBA SUNAYENSU

    April 27, 2026

    KANO TO HOST NATIONAL LAUNCH OF ECoN INITIATIVE, SET TO DRIVE INNOVATION AND INDUSTRIAL GROWTH IN NORTH-WEST

    April 16, 2026

    NewsNigeria’s Inflation Rate Climbs to 15.38% in March

    April 16, 2026

    Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika, ya musanta zargin cewa aikin samar da kamfanin jirgin saman Najeriya na ‘Nigeria Air’ da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ta ƙaddamar a zamaninta na bogi ne

    September 4, 2025
  • Education

    From Emergency to Excellence: How Kano Conquered Nigeria’s 2025 NECO Results in Three Years

    May 30, 2026

    GWAMNATIN KANO TA BAI WA DALIBAI HUTUN BABBAR SALLAH

    May 20, 2026

    KANO STUDENTS FORUM APPLAUDS GOV. YUSUF’S EDUCATION REFORMS, BACKS SECOND-TERM BID

    May 11, 2026

    AKCILS Hits 50-Year Milestone, Hosts Lavish Golden Jubilee

    April 30, 2026

    UNICEF, WHO, UNDP Donate 45 Motorcycles to Strengthen Healthcare Delivery in Kebbi

    April 29, 2026
  • Featured

    Kano State Government Organises Two-Day Retreat for Online Media Publishers in Jigawa

    January 15, 2026

    Former Kano APC Councilors Hold Special Prayers for Governor Abba Kabir Yusuf

    October 27, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    Kano Government Clarifies Position on Elders Council, Backs Its Own Initiative

    September 7, 2025
  • Health

    Zulum Directs Distribution of Free Cholera Drugs, Medical Consumables to Health Facilities

    June 1, 2026

    PUTTING CHILDREN FIRST: ONE KANO AGENDA COMMENDS DAN BELLO’S EDUCATIONAL SUPPORT INITIATIVE

    May 25, 2026

    DR. MUZAKKARI DRIVES DIGITAL HEALTH INNOVATION IN KANO STATE

    May 12, 2026

    KSCHMA EXPANDS HEALTH SCHEME TO COVER 6,000 TB PATIENTS IN KANO

    May 12, 2026

    KSCHMA Honours Governor Abba Kabir Yusuf as “Champion of Workers Progress,” Highlights AbbaCare Impact

    May 1, 2026
  • Politics

    Kwankwaso Will Ruin Your Presidential Bid, Primate Ayodele Warns Peter Obi

    June 5, 2026

    From Chibok to Dapchi and Oriire: Coincidence, Consequence, or Political Instrument?

    June 5, 2026

    ATM Gwarzo Ya Musanta Rahotannin Komawa NDC da Neman Takarar Sanata a 2027

    June 5, 2026

    Sokoto South ADC Chairman Defects To APC

    June 5, 2026

    KWANKWASO/OBI, DO THE ATTACKS ON OUR NORTHERN HEROES PLEASE YOU?

    June 5, 2026
  • Sports

    Bichi First FC Unveils Abubakar Senior as New Technical Adviser

    September 11, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    If Super Eagles Fail to Qualify for World Cup, Nigerians Will Not Forgive Us – Ahmed Musa

    September 6, 2025

    Super Falcons striker and six-time African Women’s Footballer of the Year, Asisat Oshoala, has completed her move from Bay FC to Saudi Women’s Premier League side Al Hilal

    September 3, 2025
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
BROWN PIGEON MEDIA
Home » Tsarin Kafa ’Yan Sandan Jihohi Ya Kusa Kammaluwa  Fadar Shugaban Ƙasa
Security

Tsarin Kafa ’Yan Sandan Jihohi Ya Kusa Kammaluwa  Fadar Shugaban Ƙasa

Brown Pigeon MediaBy Brown Pigeon MediaJune 5, 20263 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp Telegram Email Copy Link
Mutawakkilu Ibrahim Idris
Tsarin Kafa ’Yan Sandan Jihohi Ya Kusa Kammaluwa  Fadar Shugaban Ƙasa
Mutawakkilu Ibrahim Idris
Tsarin Kafa ’Yan Sandan Jihohi Ya Kusa Kammaluwa  Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar kafa rundunar ’yan sandan jihohi, inda ake sa ran gabatar da gyara

 

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar kafa rundunar ’yan sandan jihohi, inda ake sa ran gabatar da gyaran kundin tsarin mulki nan ba da jimawa ba domin ba da damar aiwatar da shirin.

 

Babban Ma’aikacin Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis, wadda ta haɗa manyan jami’an gwamnati da shugabannin majalisun dokoki kan batun kafa ’yan sandan jihohi.

 

Gbajabiamila ya ce an fara nazari da tattaunawa kan yadda za a kafa rundunar tun watanni uku zuwa huɗu da suka gabata bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma an samu ci gaba mai yawa a aikin.

 

Ya bayyana cewa kafa ’yan sandan jihohi ba abu ne da za a yi cikin gaggawa ba, domin akwai batutuwan kundin tsarin mulki da dokoki da dole ne a tantance su sosai kafin aiwatarwa.

 

A cewarsa, yanzu hankalin masu ruwa da tsaki ya karkata ne kan yadda za a yi gyaran kundin tsarin mulki, sannan daga baya a samar da dokokin da za su ba da cikakken iko da tsarin gudanar da rundunar.

 

Ya ƙara da cewa mafi yawan ’yan Najeriya da masu ruwa da tsaki sun amince da bukatar kafa ’yan sandan jihohi, inda muhawarar yanzu ba ta kan ko a kafa su ko a’a ba, sai dai yadda za a samar da ingantaccen tsarin doka da gudanarwa domin su yi aiki yadda ya kamata.

 

Gbajabiamila ya ce za a gabatar wa Shugaba Tinubu cikakken rahoto kan sakamakon ganawar domin ci gaba da matakan da suka dace.

 

A cewarsa, manufar kafa ’yan sandan jihohi ita ce ƙarfafa tsaron cikin gida, inganta tattara bayanan sirri daga matakin ƙasa da kuma bai wa gwamnatocin jihohi damar magance matsalolin tsaro cikin sauri da inganci.

 

Shugaba Tinubu ya sha bayyana cewa tsarin ’yan sandan jihohi na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar nan, tare da ƙara kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

Ganawar ta samu halartar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin; Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu; Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi; da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Tunji Disu, tare da sauran manyan jami’an gwamnati.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email VKontakte WhatsApp Copy Link
Previous ArticleKWANKWASO/OBI, DO THE ATTACKS ON OUR NORTHERN HEROES PLEASE YOU?
Next Article EFCC Arraigns Maiduguri CEO Over Alleged N500,000 Tricycle Fraud

Related Posts

Harin ‘Yan Bindiga A Munya: Mutum Uku Sun Mutu, An Sace Manoma Hudu

June 5, 2026

Yan Sanda 540 Sun Samu Karin Girma a Jihar Adamawa

June 2, 2026

‘YAN SANDAN ZAMFARA SUN CAFKE FITACCEN JAGORAN ’YAN BINDIGA ALI BAHAGO ƊANAKULU, SUN ƘWATO MAKAMAI

June 1, 2026

Jami’ar Sojin Ruwa Ta Girgiza Bayan Zargin Mutuwar Jami’a Mace A Lokacin Hukunci A Lagos

May 26, 2026

KAROTA TA TURA JAMI’AI 1,000 DOMIN KULA DA TSARO DA ZIRGA-ZIRGA LOKACIN BABBAR SALLAH

May 26, 2026

Rundunar ’Yan Sandan Filato Ta Cafke Mutane Shida Kan Zargin Satar Shanu Da Mallakar Bindigu Ba Bisa Ka’ida Ba

May 23, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Stay In Touch
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • Telegram
  • WhatsApp
Latest Posts

NYA- Kwankwaso’s Alliance and the Question of Northern Political Identity

By Brown Pigeon MediaJune 5, 2026

By Mutawakkilu Ibrahim Politics is often defined by alliances, negotiations, and strategic calculations. Across…

OFFICIAL STATEMENT ON THE RELOCATION OF THE NATIONAL AGENCY FOR THE GREAT GREEN WALL HEADQUARTERS TO KANO STATE

June 5, 2026

ONE KANO AGENDA HAILS FG OVER RELOCATION OF GREAT GREEN WALL AGENCY HEADQUARTERS TO KANO, URGES STATE TO LEVERAGE OPPORTUNITIES

June 5, 2026

Kano Families Return to Charcoal as Cooking Gas Prices Rise

June 5, 2026

Kwankwaso Will Ruin Your Presidential Bid, Primate Ayodele Warns Peter Obi

June 5, 2026
© 2026 Brown Pigeon Media. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.