
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa ta yi bikin rataya sabbin mukamai ga jami’ai 540 da aka kara wa girma daga mukamin Dan Sanda (Constable) zuwa Kofur (Corporal).
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Adamawa, Kabir Umar Hassan, ne ya jagoranci bikin rataya mukaman a hedikwatar rundunar da ke jihar a ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2026.
Yayin da yake jawabi ga sabbin jami’an, CP Hassan ya taya su murnar karin girman tare da tunatar da su cewa karin mukami na zuwa ne da karin nauyi da kuma karin tsammani daga shugabannin rundunar da al’umma baki daya.
Ya bukace su da su ci gaba da nuna gaskiya, kwarewa, da’a da kuma sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu domin tabbatar da amincewar da aka nuna musu.
Kwamishinan ya bayyana cewa shirin karin girman na daga cikin matakan inganta walwala da karfafa gwiwar jami’an rundunar da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya bullo da su domin yabawa jajircewa, kwazo da nagartar jami’ai wajen gudanar da aiki.
A nasa bangaren, Kofur Mary David, wadda ta yi magana a madadin sabbin jami’an da aka kara wa girma, ta gode wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, tawagar gudanarwar rundunar da kuma Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Adamawa bisa ganin sun cancanci wannan karin girma.
Ta tabbatar da cewa za su ci gaba da aiki tukuru tare da kiyaye dokoki da ka’idojin aikin ‘yan sanda domin sauke nauyin da aka dora musu.
