
Hukumar KAROTA ta tura jami’anta 1,000 zuwa muhimman wurare a faɗin jihar domin tabbatar da tsaro da kuma sauƙaƙa zirga-zirga yayin bukukuwan Babbar Sallah.
Shugaban hukumar, Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abubakar Ibrahim Sharada ya fitar.
Sanarwar ta ce hukumar ta ɗauki matakin ne domin kare lafiyar masu amfani da hanya tare da rage cunkoson ababen hawa da ake fuskanta a irin wannan lokaci na bukukuwa.
Faisal Mahmud Kabir ya ƙara da cewa hukumar ta kuduri aniyar tabbatar da zirga-zirga cikin sauƙi tare da kiyaye doka da oda a dukkanin wuraren da ake sa ran za a samu taruwar jama’a.
Muhimman wuraren da aka tura jami’an sun haɗa da masallatan Idi, manyan hanyoyi da kuma wuraren shakatawa inda ake hasashen samun cunkoso yayin gudanar da shagulgulan Sallah.
Shugaban hukumar ya kuma yi kira ga direbobi da sauran masu amfani da hanya da su bai wa jami’an KAROTA haɗin kai tare da bin dokokin hanya domin tabbatar da gudanar da bukukuwan Babbar Sallah cikin lumana da kwanciyar hankali.
