
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Laraba 27 ga watan Mayu da Alhamis 28 ga watan a matsayin ranakun hutu a faɗin Najeriya domin gudanar da shagulgulan Babbar Sallah.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dokta Magdalene Ajani ta fitar a yammacin ranar Litinin.
Sanarwar wadda aka fitar a madadin Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ta ce gwamnatin tarayya ta bayar da hutun ne domin bai wa miliyoyin musulman ƙasar damar gudanar da bukukuwan Babbar Sallah cikin walwala.
Ministan ya taya al’ummar Musulmi na cikin gida da wajen ƙasar murnar Babbar Sallah, tare da kira gare su da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa Najeriya addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin ta bayar da hutun ne domin musulman ƙasar su samu damar gudanar da shagulgulan Sallah kamar yadda sauran musulman duniya ke yi.
