
Hukumomin ƙasar Bangladesh sun hana yin layya da wani farin bijimi mai suna “Donald Trump” bayan gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa gabanin bikin Babbar Sallah.
Rahotanni sun bayyana cewa an sanya wa bijimin sunan Donald Trump ne saboda irin gashin kansa mai launin ruwan zinariya wanda ake ganin ya yi kama da na shugaban na Amurka.
An ce bijimin ya ja hankalin jama’a sosai a yankin saboda kamanninsa na ban mamaki, lamarin da ya sa mutane da dama ke tururuwar zuwa kallonsa.
Ma’aikatar Cikin Gida ta Bangladesh ta tabbatar a ranar Laraba cewa an kwashe dabbar zuwa wani wurin ajiye dabbobi domin ci gaba da kula da ita, tana mai cewa an ɗauki matakin ne saboda dalilan tsaro da kuma kare lafiyar dabbar yayin shagulgulan Babbar Sallah.
Matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, inda wasu ke ganin ya dace a kare dabbar saboda shahararta, yayin da wasu kuma ke ganin bai kamata gwamnati ta hana yin layyarta ba.
