
Yan bindiga sun kashe wani me aikin sa-kai da aka bayyana da Bawa Samari tare da wasu manoma biyu a kauyen Magure da ke gundumar Dangunu, karamar hukumar Munya a Jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun kutsa kai cikin kauyen da yammacin ranar Laraba, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya jawo asarar rayuka da kuma firgici a yankin.
Wani jami’in karamar hukumar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce bayan an kashe Bawa Samari, ‘yan bindigar sun kwashe bindigarsa kirar pump-action, sannan kuma sun yi awon gaba da wasu manoma hudu da har yanzu ba a san inda suke ba, kuma ba su tuntubi iyalansu ba. Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda kakakinta SP Wasiu Abiodun ya ce an tura tawagar hadin gwiwa zuwa yankin, kuma ana ci gaba da kokarin cafke wadanda suka aikata harin.
