
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce matakin cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta dauka ya ceci Najeriya daga durkushewar tattalin arziki tare da kafa tubalin farfadowar tattalin arzikin kasa
wannan na cikin sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai Bayo Onanuga ya fitar ranar Juma’a 29 Mayu 2026.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin gwamnoni da suka kai masa ziyarar murnar barka da Babbar Sallah da kuma cika shekara uku a kan mulki.
Tinubu ya ce, duk da cewa cire tallafin man fetur ya jawo kalubale ga jama’a, amma matakin ya zama dole domin kauce wa matsalar kuɗi da kuma dawo da daidaito ga tattalin arzikin kasar.
Ya kuma bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa a fannoni daban-daban sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda ya ce tattalin arziki na ci gaba da bunkasa tare da karuwar ayyukan raya kasa.
