
Tsohon Karamin Ministan Gidaje, Engr. Abdullahi Tijjani Gwarzo (ATM), ya karyata rahotannin da ke cewa yana shirin komawa jam’iyyar NDC ko hada kai da ’yan Kwankwasiyya domin neman kujerar Sanatan Kano ta Arewa a zaben 2027.
A cewarsa, har yanzu yana nan daram a jam’iyyar APC kuma yana ci gaba da goyon bayan gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu. Ya kuma bayyana cewa babu wata tattaunawa da ya yi da wata jam’iyyar adawa ko wani dan siyasa kan zaben 2027.
Sanarwar ta bukaci magoya baya da al’umma su yi watsi da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta, tana mai jaddada cewa Gwarzo bai canza matsayinsa ba game da takarar Sanatan Kano ta Arewa.
Labaran Brown Pigeon News