
Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da kama wani fitaccen jagoran ’yan bindiga, Ali Bahago Ɗanakulu, tare da wasu mukarrabansa a yankin Kaura Namoda. An kama su ne a ƙauyen Kasuwan Daji bisa sahihan bayanan sirri da suka kai ga samamen jami’an tsaro kan maboyar su.
A cewar kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, an kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigar a lokacin farmakin, yayin da sauran aka cafke su da ake zargi da hannu a fashi da makami da sauran munanan laifuka da suka addabi yankin. Wadanda aka kama sun haɗa da Hassan Dan Kure da Dahiru Lawali.
An ƙwato makamai daban-daban ciki har da bindigogi guda biyar, bindiga ƙirar gida (pistol), sarka ta ankwa, da babura uku. A yanzu suna tsare a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike, yayin da rundunar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da fatattakar ’yan ta’adda tare da kira ga jama’a su ci gaba da bayar da bayanan sirri.
