By Mutawakkilu Ibrahim Idris
Mataimakin babban kwamandan Hukumar Hisbah ta jihar, Dr. Mujahideen Aminudeen, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Kano.
Ya ce shirin na daga cikin kokarin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na tallafa wa marasa karfi a cikin al’umma, musamman wajen saukaka matsalolin aure.
Ya kara da cewa an yanke shawarar kara fadada shirin ne sakamakon nasarorin da aka samu a shirye-shiryen baya, wanda ya karfafa gwiwar gwamnati wajen ci gaba da zuba jari a cikinsa.
Aminudeen ya ce gwamnan ya bayar da umarnin kammala dukkan shirye-shiryen kafin karshen watan Mayu.

