
Akalla mutane 19 sun rasa rayukansu yayin da sama da 130 suka jikkata sakamakon wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.8 a ma’aunin Richter da ta afku a kudancin ƙasar Philippines a safiyar Litinin.
Hukumar kula da girgizar ƙasa ta Philippines ta bayyana cewa girgizar ta auku ne da misalin ƙarfe 7:37 na safe agogon ƙasar, a yankin tekun da ke kusa da lardin Sarangani da birnin General Santos da ke tsibirin Mindanao. Girgizar ta haddasa rushewar gine-gine da dama tare da lalata muhimman ababen more rayuwa.
Rahotanni daga yankunan da abin ya shafa sun nuna cewa gidaje, makarantu, asibitoci da wuraren kasuwanci sun gamu da mummunar ɓarna, yayin da aka samu katsewar wutar lantarki a wasu sassan birnin General Santos.
Hukumomi sun ce yawancin waɗanda suka mutu sun rasa rayukansu ne sakamakon rugujewar gine-gine, faɗuwar tarkace da kuma zaftarewar ƙasa da girgizar ta haifar. Ana kuma ci gaba da aikin bincike domin gano wasu da ake zargin sun ɓace.
Kano first

Bayan afkuwar girgizar, an fitar da gargaɗin yiwuwar tsunami a wasu yankunan Philippines da ƙasashen makwabta, lamarin da ya sa aka umarci mazauna yankunan bakin teku da su koma wurare masu tudu domin kare rayukansu. Sai dai daga baya hukumomin sa ido kan tsunami sun sanar da cewa haɗarin ya ragu sosai, kuma an janye yawancin gargaɗin.
An kuma samu jerin ƙananan girgizar ƙasa bayan babban girgizar, wasu daga cikinsu sun kai fiye da maki 6, abin da ya sa jami’an agaji suka ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana.
Ma’aikatan ceto da jami’an gwamnati sun bazama yankunan da abin ya shafa domin ci gaba da aikin ceto, taimakon gaggawa da kuma tantance girman ɓarnar da aka yi.
Ƙasar Philippines na cikin yankin da ake kira Pacific Ring of Fire, wanda ke daga cikin wuraren da ake yawan fuskantar girgizar ƙasa da aman wuta a duniya.
