
Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a jiya Juma’a sun kashe manoma 17 tare da raunata wasu 13 bayan sun mamaye gonakin da ke gundumar Goran Namaye dake a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Harin, wanda ɗaya ne daga cikin mafi muni da aka kai wa al’ummomin yankin a wannan shekarar, ya faru ne yayin da mazauna ke shirin fara komawa gonakin su don yin noma a wannan daminar.
Shaidu sun ce maharan sun mamaye gonakin da yawa, sun buɗe wuta kan manoma, sannan suka bi wasu zuwa daji.
Da yake tabbatar da lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Maradun, Hon. Sanusi Ahmed Dosara, ya ce ya samu rahoton cikin firgici.
“Da na samu wannan bayanin, na yi gaggawar sanar da dukkan hukumomin tsaro a yankin da su ɗauki matakan gaggawa da nufin hana sake afkuwar ɓarna daga masu aikata laifukan da suka aikata da nufin hana ayyukan noma,” in ji Dosara.
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana harin a matsayin wani yunƙuri na gurgunta samar da abinci da kuma hanyoyin rayuwa a yankin.
Alhaji Wada, mazaunin Goran Namaye, ya ce ya gama yi wa ma’aikatan gonarsa bayani game da tsare-tsaren aiki ne sai tsoro ya kama shi.
“Na dawo daga gona ta da ke kusa da daji inda na bayyana wa ma’aikatan yadda za su yi aiki a kanta. Na ji mutane suna ihu suna gudu zuwa garin. Daga baya, duk ma’aikatana sun dawo suka gaya mini cewa ‘yan bindiga sun kore su yayin da suke aiki a gonar,” in ji shi.
Wani mazaunin, Ɗan Inna Gora, ya ce ya ƙidaya gawawwaki akalla 17 a cikin gonakin da ke da nisan kilomita kaɗan daga garin.
Ya ƙara da cewa wasu 13 sun sami raunuka daban-daban na harbin bindiga kuma an kai su asibiti don neman kulawar likita.
Garin na Goron Namaye da al’ummomin da ke kewaye da shi a ƙaramar hukumar ta Maradun sun sha fama da hare-haren ‘yan bindaga a cikin ‘yan shekarun nan, inda galibi ana kai wa manoma hari a lokacin shuka da lokacin girbi.
Kano first

Sabbin kashe-kashen sun haifar da damuwa game da barazana ga samar da abinci a Jihar ta Zamfara
Har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da harin ba.
Duk da haka, mazauna yankin sun yi kira da a ƙara yawan sintiri da kuma tura sojoji don kare gonaki da manoman yankin.
Tuni aka gudanar da Jana’izar manoman 17 a Jiya da suka mutu bisa ga tsarin Musulunci, yayin da waɗanda suka jikkata ke karbar magani a babban asibitin da ke Maradun.
