
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya yi alkawarin cewa zai saki jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, idan ya zama Shugaban Kasa.
Obi ya bayyana cewa a ganinsa babu wani dalili da zai sa gwamnati ta ci gaba da tsare Kanu saboda kalaman suka ko zage-zage da ya rika yi ta gidan rediyon Radio Biafra.
Da yake jawabi ga wasu yan Najeriya a birnin Washington na kasar Amurka, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce idan aka zabe shi shugaban kasa, zai fifita tattaunawa da masu rajin ballewa da sauran kungiyoyin masu korafi domin warware matsalolin cikin lumana.
Kano first

A cewarsa, tattaunawa da sasanci su ne hanyoyin da suka fi dacewa wajen magance rikice-rikicen siyasa da na tsaro a kasar nan.
Nnamdi Kanu dai shi ne jagoran kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), wadda ke fafutukar kafa kasar Biafra mai cin gashin kanta.
A halin yanzu yana zaman gidan yari bayan kotu ta same shi da laifi kan wasu tuhume-tuhume da suka shafi harkokin tsaro da siyasa.
