
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ba zai taɓa bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, Netanyahu ya ce: “In dai ni ne Firamnistan Isra’ila, Iran ba za ta mallaki makamin nukiliya ba.”
Ya ƙara da cewa: “Wannan ita ce matsayar da aka cimma tsakani na da Trump kan maganar.”
Ya yi iƙirarin cewa ya kwashe shekaru 30 yana yaƙar yunƙurin Iran na mallakar makamin nukiliya.
Kano first

Netanyahu ya ce ba don ƙoƙarin da ya yi ba, da yanzu Iran ta mallaki makamin nukiliya kuma ta ruguza Isra’ila tun da ɗaɗewa.
Ya ce Iran na son ganin ta ruguza ƙasar Yahudawa, a don haka ya sadaukar da rayuwata wajen ganin wannan burin bai cika ba.
Wannan ne karon farko da Netanyahu ya yi magana bayan da Trump ya ce an cimma matsaya da Iran, kuma ya fasa kai mata hare-haren da ya yi niyyar ƙaddamarwa a daren Alhamis.
