
Jam’iyyar NNPP ta zargi tsohon ɗan takarar shugaban ƙasarta a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ci gaba da yi mata katsalandan a harkokinta duk da cewa bashi da alaka da ita a yanzu.
Jam’iyyar NNPP ta yi wannan zargi a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Mista Ogini Olaposi, ya fitar a jihar Lagos.
Kano first

Bayanai sun rawaito NNPP na cewa Kwankwaso na ci gaba da yin tasiri a jam’iyyar ta hanyar amfani da wasu magoya bayansa da ake zargin ya bari a cikinta bayan ficewarsa.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yana kokarin mamaye jam’iyyar NDC kamar yadda ya yi mata.
NNPP ta kuma yi ikirarin cewa ƙarfin siyasar Kwankwaso a jihar Kano ya ragu matuƙa, tana mai cewa da dama daga cikin manyan magoya bayansa sun koma jam’iyyar APC.
