Hu

kumar Bunƙasa Kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA), tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), sun gudanar da taron wayar da kai da haɗin gwiwa ga ƙananan da matsakaitan masana’antu (MSMEs) a faɗin Jihar Katsina.
Taron wanda aka gudanar a ranar Alhamis, 11 ga Yuni, 2026, a Cibiyar Taro ta Education Resource Centre da ke Katsina, ya mayar da hankali ne kan muhimmancin bin ƙa’idojin hukumomi domin bunƙasa kasuwanci da masana’antu a jihar.
Taken taron shi ne: “Sauƙaƙa Bin Ka’idojin Hukumomi Domin Haɓaka MSMEs a Jihar Katsina.”
A jawabinsa, Darakta Janar na KASEDA, Dakta Babangida Kabir Ruma, ya bayyana cewa shirin na da nufin wayar da kan masu sana’o’i da ‘yan kasuwa kan hanyoyin samun rajista, lasisi da kuma bin ƙa’idojin NAFDAC domin inganta kayayyakin da suke samarwa tare da ƙara musu damar shiga manyan kasuwanni.
Kano first

Shi ma Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, wanda yake ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziki da ƙarfafa matasa da mata masu sana’o’i, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau da zai taimaka wa ƙananan da matsakaitan masana’antu su bunƙasa.
Shirin ya haɗa masu sana’o’i, masu ƙananan masana’antu, ƙungiyoyin kasuwanci da sauran masu ruwa da tsaki, inda aka tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen sauƙaƙa bin ƙa’idojin hukumomi da kuma ƙara ingancin kayayyakin da ake samarwa a jihar.
An yi fatan cewa irin wannan haɗin gwiwa tsakanin KASEDA da NAFDAC zai ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin Jihar Katsina.
