
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da wasu sabbin naɗe-naɗe tare da sauya wa wasu daga cikin masu ba shi shawara mukamai, a wani mataki da gwamnatin jihar ta ce na da nufin ƙara inganta tafiyar da gwamnati da kuma bunƙasa ayyukan yi wa al’umma hidima.
Sanarwar ta fito ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya bayyana cewa an soke mukaman Mai Ba da Shawara kan Harkokin Cikin Gida da kuma Mai Ba da Shawara kan Ofishin Gwamnati na Abuja, inda aka mayar da waɗanda ke riƙe da mukaman zuwa wasu sababbin ayyuka.
Daga cikin sauye-sauyen da aka yi, an naɗa Habiba Mustapha Barwa a matsayin Mai Ba da Shawara kan Ayyuka na Musamman na Mata, yayin da Umar Uba Akawu ya zama Mai Ba da Shawara a Ofishin Majalisar Zartarwa kan Harkokin Siyasa.
Kano first

Haka kuma, Akibu Isa Murtala ya koma fannin kula da ma’aikata, Ibrahim Adam ya karɓi harkokin sadarwa na zamani, yayin da Nasiru Isa Dikko ya koma bangaren tallafawa da bunƙasa rayuwar al’umma.
A cikin sabbin naɗe-naɗen, gwamnan ya amince da naɗin Bello Nuhu Bello a matsayin Mai Ba da Shawara kan Mulki a Ofishin Gwamna, Ahmed Muhammad Aruwa a matsayin Mai Ba da Shawara kan Yaɗa Labarai, Buhari Sule Kura kan Harkokin Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu, da Yahuza Ado Yankaba a matsayin Mai Ba da Shawara kan Tashoshin Mota.
Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Ahmed Tijjani Musa, Ibrahim Hamisu Rimi, Mustapha Abdullahi Rabiu Kura, Injiniya Bashir Abdullahi Kutama, Naziru Abdullahi Karaye da Tahir Ado Rabi’u.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa sauye-sauyen na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin daidaita ayyukan hukumomi da manufofin gwamnatin jihar, tare da tabbatar da ingantaccen aiki da kyakkyawan shugabanci.
Ya kuma buƙaci sabbin waɗanda aka naɗa da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, ƙwarewa da jajircewa, domin tabbatar da ci gaban Jihar Kano da kyautata rayuwar al’ummarta.
Brown Pigeon News ta fahimci cewa wannan sabon tsarin naɗe-naɗen na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan gudanarwa da kuma haɓaka aiwatar da shirye-shiryen ci gaban al’umma a faɗin Kano.
