
Rahotanni daga Abuja na cewa fitaccen mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya suma yayin wata arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga a dandalin Unity Fountain.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a yayin zanga-zangar ranar dimokuraɗiyya da aka shirya domin nuna rashin jin daɗi kan matsalar tsaro da tsadar rayuwa da kuma abin da masu zanga-zangar suka kira da rashin ingantaccen shugabanci.
Kano first

Shaidun gani da ido sun ce jami’an tsaro sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa taron, lamarin da ya janyo ruɗani, yayin da masu zanga-zangar suka rika neman mafaka.
Rahotannin sun kara cewa Sowore ya farfaɗo yayin da ake daukarsa daga wurin taron cikin wata mota.
Daga bisani kuma an garzaya da shi wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba domin a duba lafiyarsa.
