
BROWN PIGEON MEDIA
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa babu wani bambanci tsakanin ‘ya’yansa da yaran da ke zaune a gidan marayu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai gidan marayu da ke Nassarawa, inda aka shirya walimar Sallah domin sanya farin ciki a zukatan yaran.
Ya ce nan gaba za a iya samun shugabanni, malamai da sauran manyan mutane daga cikin waɗannan yara, la’akari da ilimi da kyakkyawar tarbiyyar da suke samu a gidan marayun.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma yaba da gudummawar da mawadata da kamfanoni ke bayarwa wajen tallafawa rayuwar marayun, tare da yin kira ga sauran masu hannu da shuni da su shiga cikin wannan aikin alheri domin samun lada a duniya da lahira.
Haka kuma, ya gode wa shugabannin gidan marayun bisa yadda suke riƙe amanar kula da yaran, tare da samar musu da Kyakkyawar kulawa.
A ƙarshen ziyarar tasa, gwamnan ya zagaya sassan gidan marayun, inda ya gaisa da yaran tare da cin abinci da su a matsayin wani ɓangare na walimar Sallah.
Jaridar Brown pigeon media ta ruwaito cewa yaran sun kar-kare walimar sallar cikin nishadi, farin ciki da raye-raye da wasanni irin su hawa lilo da guje -guje.
