
Majalisar wakilai ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa rundunar ‘yansandan jihohi a Najeriya. Newspapers
An amince da kudirin ne a zaman majalisar na ranar Alhamis bayan ‘yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da shi.
Kano first

Amincewar da majalisar ta yi da kudirin na daga cikin muhimman matakan da ake dauka wajen sauya tsarin tsaro a kasar, inda jihohi za su samu damar kafawa da gudanar da rundunonin ‘yansandansu tare da hadin gwiwa da hukumomin tsaron tarayya.
