
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 23 ga watan Yuni na kowace shekara domin wayar da kan al’umma kan halin da zawarawa ke ciki da kuma ƙalubalen da suke fuskanta.
Daga cikin matsalolin da zawarawa ke fuskanta akwai talauci, rashin samun haƙƙin gado, wariya, cin zarafi da kuma ɗaukar nauyin iyali su kaɗai bayan rasuwar mazajensu.
A wannan rana, ana kira ga gwamnatoci, ƙungiyoyi da al’umma da su tallafa wa zawarawa tare da kare haƙƙoƙinsu domin su samu rayuwa mai inganci da mutunci.
#RanarZawarawaTaDuniya #InternationalWidowsDay #BrownPigeonNewsPublications
