
Gwamnatin tarayya ta musanta jita-jitar shirin soke hukumar kula da hukumar shirya jarrabawa ta nazarin harshen larabci da addinin musulunci ta NBAIS
Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Folasade Boriowo, ta fitar, ma’aikatar Ilimi ta tarayya ta ce anja hankalin hukumar ga wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke nuna cewa gwamnati tare da majalisar dokoki ta kasa na shirin soke hukumar.
Kano first

Hukumar NBAIS , hukuma ce da ke da alhakin tsarawa da bayar da takardar shaidar nazarin harshen larabci da addinin musulunci a Najeriya.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa NBAIS har yanzu hukuma ce da gwamnati ta amince da ita a matsayin cibiyar gudanar da jarrabawa da ba da takardun shaida a tsarin ilimin Najeriya.
