
Shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa tare da manyan jagororin jam’iyyar na gudanar da wani taro a otal ɗin Continental da ke Abuja domin bayyana mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Matakin na zuwa ne bayan watanni ana raɗe-raɗin cewa Shugaba Tinubu na iya sauya Shettima tare da zaɓar wani Kirista daga Arewacin Najeriya a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Majiyoyi daga cikin manyan jagororin APC da ke halartar taron sun tabbatar cewa Shugaba Tinubu ya sake zaɓen Shettima a matsayin abokin takararsa, kuma ana sa ran jam’iyyar za ta sanar da hakan a hukumance a yau.
Ana ci gaba da jiran ƙarin bayani kan sakamakon taron da kuma sanarwar da jam’iyyar za ta fitar.
