
Daga Mutawakkilu Ibrahim Idris
Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, kuma Mataimakin Mai Tsawatar da Marasa Rinjaye a Majalisar, Sanata Rufai Sani Hanga, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NDC.
A cikin wasiƙar murabus mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Agusta, 2026, wadda ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazaɓar Dakata da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano, Sanata Hanga ya bayyana cewa murabus ɗinsa ya fara aiki nan take.
Sanatan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan nazari da tunani mai zurfi, yana mai bayyana cewa ya bar jam’iyyar ne domin mayar da hankali kan wasu muhimman al’amuran rayuwarsa da kuma ci gaban aikinsa.
Ya kuma gode wa shugabannin jam’iyyar daga matakin mazaɓa zuwa kwamitin gudanarwa da daukacin mambobin NDC bisa irin goyon baya, damar siyasa da haɗin kai da suka ba shi a tsawon lokacin da yake cikinta.
Haka kuma, Hanga ya buƙaci a cire sunansa daga kundin rajistar mambobin jam’iyyar a matakin mazaɓa, tare da tabbatar da cewa ya mayar da katin shaidarsa na zama ɗan jam’iyyar NDC.
A ƙarshe, Sanatan ya yi wa jam’iyyar da daukacin mambobinta fatan alheri da nasara a dukkan ayyukansu na gaba.
Sai dai, duk da sanar da ficewarsa daga NDC, Sanata Rufai Sani Hanga bai bayyana ko yana da shirin komawa wata jam’iyyar siyasa ba.
