
Gwamnatin ƙasar Saudi Arabia ta ɗauki wani sabon mataki na inganta jin daɗin alhazai yayin aikin Hajjin shekarar 2026, inda ta maye gurbin tsofaffin na’urorin sanyaya waje guda 45,600 da sabbin na’urori masu inganci a tantunan Mina.
Rahotanni sun bayyana cewa an shigo da sabbin na’urorin ne daga ƙasar Australia domin taimakawa wajen rage raɗaɗin zafin rana da alhazai ke fuskanta yayin gudanar da aikin Hajji.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da mahukuntan Saudiyya ke ci gaba da faɗaɗa ayyukan more rayuwa da kuma inganta wuraren ibada domin samar da sauƙi, kariya da walwala ga miliyoyin musulman da ke zuwa ƙasa mai tsarki daga sassa daban-daban na duniya.
Mina na daga cikin muhimman wuraren da alhazai ke sauka da kwana yayin gudanar da ibadun Hajji. Wurin na karɓar miliyoyin mahajjata a duk shekara, musamman a lokacin Arfa da Jifan Shaidan.
A duk shekara, dubban tantuna kan cika da alhazai da ke hutawa tare da gudanar da ibadunsu cikin yanayi mai cike da taron jama’a da tsananin zafi.
Masana sun bayyana cewa girke wadannan sabbin na’urorin sanyaya iska zai taimaka ƙwarai wajen rage tasirin zafi, musamman duba da yadda yanayin zafi ke ƙaruwa a lokacin bazara a ƙasar Saudiyya.
Haka kuma, ana kallon wannan shiri a matsayin wani ɓangare na manufofin Saudiyya na ci gaba da inganta aikin Hajji tare da tabbatar da jin daɗi da lafiyar alhazai yayin gudanar da ibadunsu cikin kwanciyar hankali.
