
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami tare da matarsa da ɗansa, zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2026.
Hukumar Economic and Financial Crimes Commission EFCC na tuhumar su da laifuka guda 16 da suka haɗa da haɗa baki da kuma ɓoye kuɗaɗen haram da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 8.7.
A zaman kotun da aka gudanar ranar 22 ga watan Mayu, lauyan masu gabatar da ƙara, J. S. Okutepa, ya bayyana cewa an shirya ci gaba da sauraron shari’ar, sai dai lauyoyin masu kare waɗanda ake tuhuma sun aika wasiƙar neman a ɗage zaman kotun.
Masu gabatar da ƙarar sun nuna damuwa kan yawaitar ɗage zaman shari’ar, suna mai cewa hakan na iya kawo tsaiko wajen gudanar da shari’ar cikin lokaci.
Mai shari’a, Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa rashin halartar babban lauyan masu kare waɗanda ake tuhuma bai kamata ya hana ci gaba da sauraron shari’ar ba, domin akwai wasu lauyoyi a ofishinsa da za su iya wakiltarsa.
Sai dai duk da haka, kotun ta amince da buƙatar ɗagewar, inda mai shari’ar ta ce doka ta bai wa ɓangarorin damar neman ɗage zaman a irin wannan yanayi.
Daga nan ne kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2026.
