
Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya nada sabbin dagatai guda uku da suke daga yankin gundumar kunya a karamar hukumar Minjibir.
An nada Shamsu Aminu a matsayin dagacin Garke yayin da aka nada Abdulhamid Muhd a matsayin dagacin garinTtsage sai kuma Malam Nadabo Lawan a matsayin dagacin garin Dogon kawo dake karamar hukumar doguwa.
bayan kammala nadin nasu mai maraba sarki Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya hore sui dasu zauna lafiya da al’ummarsu su kuma sanya idanu kan harkokin tsaro lafiya da ilimi a garuruwansu.
A nasu jawaban daban daban sabon dagacin garin dogon kawo a karamar hukumar doguwa Malam Nadabo Lawan ya bayyana farin cikinsa bisa nadashi da mai maraba sarki Kano yayi a matsayin dagacin garin ya kuma ce zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya da rikon amana tare da kira ga al’ummar garin nasa dasu bashi hadin kai da goyon baya a kowane lokaci.
