
Makabartar Baki’a na daga cikin tsofaffin makabartu a Musulunci, kuma tana kusa da Al-Masjid an-Nabawi dake birnin Madina.
Masana tarihi sun bayyana cewa an fara amfani da makabartar tun zamanin Annabi Muhammad (SAW), inda aka binne sahabbai, iyalan Annabi da sauran fitattun musulmai da dama.
Daga cikin wadanda aka fi sani da aka binne a Baki’a akwai Uthman ibn Affan da sauran sahabbai da tabi’ai masu yawa.
Makabartar Baki’a na da muhimmanci sosai a tarihin Musulunci, kasancewar Annabi Muhammad (SAW) ya kasance yana ziyartarta tare da yi wa wadanda aka binne a cikinta addu’a.
Zamu cigaba da kawo muku wuraren tarihi daga kasar Saudiyya tare da wakilinmu dake can yanzu haka Mubarak Auwal Unguwa Uku.
