
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa jam’iyyar na da ingantattun hanyoyin da za ta bi wajen sasanta saɓanin da ya kunno kai a wasu jihohi bayan gudanar da zaɓukan fidda gwani gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, inda ya tabbatar da cewa shugabancin jam’iyyar na sane da koke-koke da rashin jituwar da suka biyo bayan zaɓukan fidda gwani a wasu sassan ƙasar nan.
A cewarsa, APC jam’iyya ce mai girma da ke da tsarin sulhu da warware rikice-rikice cikin lumana, yana mai cewa shugabannin jam’iyyar za su yi aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin mambobinta.
Shugaban ya jaddada cewa duk da matsalolin da suka taso, jam’iyyar za ta ci gaba da ƙarfafa demokuraɗiyya cikin gida tare da bai wa kowane mamba damar bayyana ra’ayinsa cikin adalci da gaskiya.
Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su guji furta kalaman da za su iya ƙara rura wutar rikici, yana mai cewa haɗin kai ne kaɗai zai bai wa APC damar samun nasara a zaɓen 2027.
Wasu daga cikin mambobin jam’iyyar dai sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwani a wasu jihohi, lamarin da ya haifar da rabuwar kai da zargin nuna son kai a cikin jam’iyyar.
