Daga. Brown pigeon media
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama mutane shida kan harin da ƴan daba suka kai kasuwar wayoyi ta Farm Centre bayan rikicin da ya barke a unguwar Gyadi Gyadi a ranar Litinin din data gabata
wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Litinin 27 ga Afrilu, 2026 kamar yadda brown pigeon ta rawaito
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 1:20 na rana da bayanan cewa wasu da ake zargin ’yan daba sun taru domin tada rikici a Gyadi Gyadi.
Bayan isar jami’an sintiri wurin, sun tarar da tarzoma har an lalata motar daukar marasa lafiya tare da yunƙurin kai hari wasu wurare.
Daga bisani wadanda ake zargin sun tsere zuwa kasuwar Farm Centre inda suka yi yunƙurin shiga shaguna domin wawashe kaya kafin rundunar ta tura karin jami’ai suka tarwatsa su tare da kama mutane shida.
Ya ce, ana ci gaba da bincike domin kamo sauran wadanda suka tsere.
Sanarwar ta ce, Kwamishinan ƴan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori, ya ce, ba za su lamunci duk wani yunƙuri na kawo tasgaro ga zaman lafiyar Kano ba, tare da shan alwashin duk masu harkar daba za su ɗaɗana kuɗarsu.

