Wata gobara mai tsanani ta tashi a kasuwar ’yan katako da ke kan hanyar Maganda a cikin birnin Kano, lamarin da ya jefa ’yan kasuwa da mazauna yankin cikin firgici.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne da sanyin safiya, inda wutar ta bazu cikin sauri sakamakon yawan katako da sauran kayayyakin da ke saurin kamawa da wuta a kasuwar.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an rika ganin harshen wuta yana tashi sama tare da hayaki mai kauri wanda ya mamaye sararin samaniya a yankin.
Jami’an kashe gobara sun isa wurin domin kokarin shawo kan lamarin tare da hana yaduwar gobarar zuwa wasu sassa.
Zu zuwa yanzu dai ba a tabbatar da yawan asarar da aka yi ba.
— Brown Pigeon News

