Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Business
  • Education
  • Featured
  • Health
  • Politics
  • Sports
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram
Facebook Instagram TikTok
BROWN PIGEON MEDIA
SUBSCRIBE
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    FEDERAL GOVERNMENT SUSPENDS PROPOSED WAEC, NECO REGISTRATION FEE HIKE

    July 13, 2026

    FG: FANNIN MA’ADANAI YA JAWO JARIN DALA BILIYAN 3 CIKIN SHEKARU UKU

    June 18, 2026

    GWAMNATIN TARRAYYA TA MUSANTA SHIRIN SOKE HUKUMAR NBAIS

    June 18, 2026

    DEMOCRACY DAY SPEECH: OUR GENERATION MUST SECURE PROSPERITY 

    June 12, 2026

    Senator Barau Reaffirms ECOWAS Parliament’s Commitment to Regional Unity at Commissioning of New ECOWAS Headquarters

    July 3, 2026

    DA DUMI-DUMI: Starmer ya yi Murabus Daga Mukamin Firaministan Birtaniya

    June 22, 2026

    NETANYAHU YA SHA ALWASHIN HANA IRAN MALLAKAR MAKAMIN NUKILIYA

    June 13, 2026

    Girgizar Ƙasa Mai Ƙarfi Ta Hallaka Mutane a Philippines, Ana Fargabar Tsunami a Wasu Ƙasashe

    June 8, 2026

    KANO INTELLECTUALS FORUM INAUGURATED TO HARNESS ACADEMIC EXPERTISE FOR SOCIOECONOMIC DEVELOPMENT — WAIYA

    October 6, 2026

    THE COALITION OF YOUNG PATRIOTIC IMAMS OF JUMA’AT MOSQUES IN NORTHERN NIGERIA HONOURS WAIYA WITH “GWANI” TITLE

    October 4, 2026

    WAIYA YA HALARCI KHATAMAR SAUKAR ALƘUR’ANI MAI GIRMA GUDA 3,313

    October 4, 2026

    52 Kano Residents Receive Free Urological Surgeries in Saudi-Supported Medical Outreach

    October 4, 2026
  • Business

    KASEDA TA GUDANAR DA SHIRIN WAYAR DA KAI GA MSMEs KAN KA’IDOJIN NAFDAC A JIHAR KATSINA

    June 12, 2026

    Dangote Industrialising Africa– NCCIMA DG

    May 17, 2026

    INEC TA BUKACI MASU RIJISTAR KATIN ZABE A KANO DA SU JE SU DUBA SUNAYENSU

    April 27, 2026

    KANO TO HOST NATIONAL LAUNCH OF ECoN INITIATIVE, SET TO DRIVE INNOVATION AND INDUSTRIAL GROWTH IN NORTH-WEST

    April 16, 2026

    NewsNigeria’s Inflation Rate Climbs to 15.38% in March

    April 16, 2026
  • Education

    WAIYA URGES STUDENTS TO UPHOLD DISCIPLINE, PATRIOTISM AT INDEPENDENCE ANNIVERSARY

    October 2, 2026

    WAIYA COMPLETES PhD VIVA VOCE, EARNS NEW ACADEMIC DISTINCTION

    September 22, 2026

    Gov. Yusuf Reaffirms Education Priority, Commends Al-Istiqama University’s Impact

    September 19, 2026

    KANO RANKS FIRST IN EDUCATION SPENDING, SECOND IN CLIMATE GOVERNANCE

    September 13, 2026

    KANO GOVERNMENT INAUGURATES 14-MEMBER COMMITTEE TO OVERSEE HANDOVER OF SORTED RANO FACILITIES TO FEDERAL POLYTECHNIC

    September 11, 2026
  • Featured

    Kano State Government Organises Two-Day Retreat for Online Media Publishers in Jigawa

    January 15, 2026

    Former Kano APC Councilors Hold Special Prayers for Governor Abba Kabir Yusuf

    October 27, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    Kano Government Clarifies Position on Elders Council, Backs Its Own Initiative

    September 7, 2025
  • Health

    NORTH-WEST DEVELOPMENT COMMISSION TEAMS UP WITH DALA ORTHOPAEDIC HOSPITAL TO EASE MEDICAL COSTS

    August 1, 2026

    Kano Government Targets Maternal Mortality with 484 New Mini-Ambulances for Rural Wards

    June 19, 2026

    Gwamnatin Kano Ta Sayi Ƙananan Motocin Asibiti 484 Domin Taimaka wa Mata Masu Juna Biyu – Kwamishinan Lafiya

    June 19, 2026

    SHAYAR DA NONON UWA ZALLA NA KARE YARA DAGA CUTUTTUKA — KWAMISHINAN LAFIYA

    June 16, 2026

    Hukumar Kula da Asibitocin Kano Ta Tsaurara Matakai Kan Rashin Zuwa Aiki bisa Jadawalin Ayyuka

    June 11, 2026
  • Politics

    TINUBU ABBA GIDA GIDA OYOYO 2027 DECLARES FULL SUPPORT FOR APC, APPOINTS WAIYA AS PATRON

    October 6, 2026

    WAIYA RECEIVES AHMAD S. ARUWA ON COURTESY VISIT

    September 29, 2026

    Dan Agundi Congratulates 21 New Kano Special Advisers, Urges Commitment to APC’s Success

    September 26, 2026

    KOTU TA SOKE TSAYAR DA PANTAMI A MATSAYIN ƊAN TAKARAR PDP A GOMBE

    September 24, 2026

    BARAU, ABBA AND THE NEW POLITICAL REALITY: WHY THE NOISE FROM SIDELINES WILL NOT DEFINE THEM.

    September 19, 2026
  • Sports

    Bichi First FC Unveils Abubakar Senior as New Technical Adviser

    September 11, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    If Super Eagles Fail to Qualify for World Cup, Nigerians Will Not Forgive Us – Ahmed Musa

    September 6, 2025

    Super Falcons striker and six-time African Women’s Footballer of the Year, Asisat Oshoala, has completed her move from Bay FC to Saudi Women’s Premier League side Al Hilal

    September 3, 2025
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
BROWN PIGEON MEDIA
Home » KARE MANUFAR MULKI: DALILIN DA YA SA JIHAR KANO BA ZA TA IYA LAMUNTAR MAKARKASHIYAR SIYASA BA A WANNAN LOKACI
News

KARE MANUFAR MULKI: DALILIN DA YA SA JIHAR KANO BA ZA TA IYA LAMUNTAR MAKARKASHIYAR SIYASA BA A WANNAN LOKACI

Brown Pigeon MediaBy Brown Pigeon MediaJune 21, 20265 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp Telegram Email Copy Link
Mutawakkilu Ibrahim Idris
KARE MANUFAR MULKI: DALILIN DA YA SA JIHAR KANO BA ZA TA IYA LAMUNTAR MAKARKASHIYAR SIYASA BA A WANNAN LOKACI

 

Mutawakkilu Ibrahim Idris
KARE MANUFAR MULKI: DALILIN DA YA SA JIHAR KANO BA ZA TA IYA LAMUNTAR MAKARKASHIYAR SIYASA BA A WANNAN LOKACI

Daga Mohammed Babagana Abubakar

 

A kowace al’umma mai tsarin dimokuradiyya, gasa ta siyasa da muhawarar jama’a suna daga cikin ginshiƙan shugabanci nagari. Jihar Kano, wadda ta yi fice wajen wayewar siyasa da ƙwarewar al’amuran jama’a, ta kasance cibiyar tattaunawa da muhawara kan harkokin mulki. Sai dai kuma akwai lokutan da ya zama wajibi a fifita muradun al’umma gaba ɗaya fiye da muradun wasu tsirarun mutane ko ƙididdigar siyasa. Wannan ne irin lokacin da Kano ke ciki a yau.

 

A ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, jihar Kano ta shiga wani sabon zamani na mayar da hankali kan kyakkyawan shugabanci, gyaran cibiyoyi, bunƙasa ababen more rayuwa, da inganta walwalar jama’a. Tun bayan hawansa mulki, gwamnatin ta himmatu wajen dawo da amincewar jama’a ga gwamnati tare da tabbatar da cewa cigaba ya isa ga al’ummomin da ke cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar. A yau, ana ganin sakamakon waɗannan ƙoƙari a fannoni daban daban kamar ilimi, lafiya, tsaro da kuma ƙarfafa matasa.

 

Yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar yin garambawul a majalisar zartarwa ta jihar, abu ne na al’ada a tsarin mulki a ga masu ruwa da tsaki suna nuna sha’awa da fata. Garambawul a gwamnati wani ɓangare ne na shugabanci wanda ake amfani da shi domin ƙara inganci da bunƙasa ayyukan gwamnati. Amma irin waɗannan matakai ya kamata su kasance bisa kimanta aiki da nasarorin da aka samu, ba wai saboda matsin lamba na siyasa ko neman biyan bukatun wasu mutane ba.

 

Abin takaici, wasu alamu sun nuna cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ke ƙoƙarin amfani da wannan yanayi domin ciyar da muradunsu na kashin kai gaba. Rahotannin yakin neman mukamai a bayan fage, amfani da wakilai wajen yada manufofi, da kuma wasu dabaru na matsin lamba sun fara karkatar da hankali daga muhimman ayyukan gwamnati. Duk da cewa kowane ɗan ƙasa na da damar neman mukamin gwamnati, bai kamata a mayar da mulki wata fafatawa ta neman kujeru ba har ta kai ga kawo cikas ga cigaban da ake samu.

Ɗaya daga cikin ma’aikatun da suka fi daukar hankalin jama’a a wannan lokaci ita ce Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, ƙarƙashin jagorancin Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya. Tun bayan naɗinsa, an shaida gagarumin sauyi a yadda ma’aikatar ke gudanar da harkokin sadarwa da hulɗa da jama’a. Bisa gogewarsa a harkokin ƙungiyoyin fararen hula da aiki a matakin al’umma, Waiya ya taimaka wajen mayar da ma’aikatar wata gada tsakanin gwamnati da talakawa, maimakon ta kasance kawai cibiyar fitar da sanarwar gwamnati.

 

Baya ga harkokin sadarwa, ma’aikatar ta taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa shirye shiryen da suka shafi zaman lafiya da tsaron al’umma. Shirye shirye irin su Safe Corridor Initiative sun nuna ƙudirin gwamnati na magance tushen matsalolin tsaro ta hanyoyin zaman lafiya, wayar da kan matasa da sake gyara rayuwar waɗanda ke cikin haɗari. Haka kuma, ƙarfafa tsarin tsaro na al’umma da haɗa matasa cikin ayyukan tsaro ya ƙara taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a sassa daban daban na jihar.

 

Wadannan nasarori ba sa nufin cewa babu wanda za a iya tantance aikinsa ko sauya shi. A tsarin dimokuradiyya, alhaki da yin aiki yadda ya kamata suna da muhimmanci. Amma abin da ya kamata ya kasance ma’aunin hukunci shi ne nagartar aiki da sakamakon da aka samu. Sauya shugabanci mai inganci domin kawai gamsar da wasu bukatun siyasa ko samar wa wasu dandali na cimma burinsu na gaba na iya janyo koma baya ga ayyukan da ake gudanarwa da kuma ci gaban cibiyoyi.

 

Ƙarfin kowace gwamnati ba ya ta’allaka ne kawai ga hangen nesan shugabanta ba, har ma da ƙwarewa, jajircewa da amincin mutanen da aka ɗora wa alhakin aiwatar da wannan hangen nesa. Kyakkyawan shugabanci na buƙatar daidaito, ci gaba da tsare tsare, da kuma kiyaye ƙwarewar da aka tara tsawon lokaci. Duk wani sauyi da ya samo asali daga son zuciya ko matsin lambar siyasa maimakon tantance aiki na iya raunana cibiyoyin da ake buƙata domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna a lokuta da dama cewa yana fifita muradun jama’a sama da anfani na siyasa. Mayar da hankalin gwamnatinsa kan ilimi, lafiya, tsaro da walwalar al’umma ya nuna cewa manufarsa ita ce samar da sakamako mai ɗorewa ga al’umma. Kare wannan mayar da hankali zai kasance muhimmi yayin da gwamnati ke shirin shiga sabon mataki na aiwatar da manufofinta.

 

A wannan muhimmiyar gaɓa, ya zama wajibi ga masu ruwa da tsaki, magoya baya da sauran al’umma su guji duk wani yunƙuri na karkatar da hankali daga harkokin cigaba. Neman mukami hakki ne na kowane ɗan ƙasa, amma bai kamata ya zama sama da muradun jama’a ba. Ya kamata tattaunawa ta mayar da hankali kan yadda za a ƙara bunƙasa jihar, ƙarfafa cibiyoyi, samar da damammaki ga matasa, da kuma inganta rayuwar al’umma baki ɗaya.

 

A ƙarshe, nasarar kowace gwamnati tana dogara ne da yadda take iya ci gaba da aiwatar da manufofinta ba tare da shagaltuwa da hayaniyar siyasa ba. Jihar Kano ba za ta iya ɗaukar nauyin rashin kwanciyar hankali ko wasu dabarun siyasa da za su iya kawo cikas ga cigaban da ake samu ba. Abin da ya kamata ya kasance a gaba shi ne kare manufa, tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu, da kuma ci gaba da aiwatar da manufofin da za su amfani al’ummar Kano baki ɗaya.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email VKontakte WhatsApp Copy Link
Previous ArticleGwamna Abba Ya Ba da Umarnin Bincike Kan Rasuwar Dalibar St. Louis, Maimuna Nihal
Next Article SILENT ACHIEVEMENTS, LOUD IMPACT: ASSESSING THE FOOTPRINTS OF IBRAHIM WAIYA IN THE PRESENT ADMINISTRATION

Related Posts

KANO INTELLECTUALS FORUM INAUGURATED TO HARNESS ACADEMIC EXPERTISE FOR SOCIOECONOMIC DEVELOPMENT — WAIYA

October 6, 2026

THE COALITION OF YOUNG PATRIOTIC IMAMS OF JUMA’AT MOSQUES IN NORTHERN NIGERIA HONOURS WAIYA WITH “GWANI” TITLE

October 4, 2026

WAIYA YA HALARCI KHATAMAR SAUKAR ALƘUR’ANI MAI GIRMA GUDA 3,313

October 4, 2026

52 Kano Residents Receive Free Urological Surgeries in Saudi-Supported Medical Outreach

October 4, 2026

NIGERIA: A NATION OF HOPE, STRENGTH AND POSSIBILITY

October 4, 2026

Waiya Celebrates Nigeria’s 66th Independence Anniversary, Calls for Unity and Peace

October 1, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Stay In Touch
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • Telegram
  • WhatsApp
Latest Posts

KANO INTELLECTUALS FORUM INAUGURATED TO HARNESS ACADEMIC EXPERTISE FOR SOCIOECONOMIC DEVELOPMENT — WAIYA

By Brown Pigeon MediaOctober 6, 2026

The Kano State Commissioner for Information and Internal Affairs, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, PhD…

TINUBU ABBA GIDA GIDA OYOYO 2027 DECLARES FULL SUPPORT FOR APC, APPOINTS WAIYA AS PATRON

October 6, 2026

KANO FIRST FORUM PETITIONS COMMISSIONER OF POLICE AGAINST ALH. AMINU BABBA DAN AGUNDI OVER ACTIONS CAPABLE OF INVITING VIOLENCE

October 5, 2026

THE COALITION OF YOUNG PATRIOTIC IMAMS OF JUMA’AT MOSQUES IN NORTHERN NIGERIA HONOURS WAIYA WITH “GWANI” TITLE

October 4, 2026

WAIYA YA HALARCI KHATAMAR SAUKAR ALƘUR’ANI MAI GIRMA GUDA 3,313

October 4, 2026
© 2026 Brown Pigeon Media. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.