
Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun ɗauki ɗan gwagwarmaya kuma mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore zuwa Gidan Yarin Kuje bayan zaman Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin.
Rahotanni sun nuna cewa Mai Shari’a Mohammed Umar ya umarci a tsare Sowore a Gidan Yarin Kuje har zuwa ranar Laraba, bayan da kotun ta soke belinsa kan rashin halartar zaman kotu da ya gabata. Bayan kammala zaman kotun ne jami’an DSS suka karɓe shi domin aiwatar da umarnin kotun.

Haka kuma, kotun ta yi watsi da bukatar da Sowore ya gabatar na neman mai shari’ar ya janye daga sauraron shari’arsa, inda ta bayyana cewa hujjojin da aka gabatar ba su isa su tabbatar da zargin son kai ba.
Lamarin ya janyo martani daga magoya bayansa da masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, yayin da ake ci gaba da sauraron shari’ar da DSS ta shigar a kansa.
Brown Pigeon News Publications.
