
Daga Mutawakkilu Ibrahim Idris
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada aniyar Gwamnatin Jihar Kano na ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙungiyoyin na al’umma domin bunƙasa tsaro, zaman lafiya da ci gaban jihar.
Waiya ya bayyana hakan ne bayan wata ziyara da ya kai ofishin ƙungiyar Gyara Kayanka reshen Ƙaramar Hukumar Kumbotso, ƙungiyar da ke taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa hukumomin tsaro da kuma sasanta rikice-rikicen al’umma a faɗin jihar.
Ya bayyana cewa kafin ziyarar, ya gudanar da muhimman tattaunawa da shugabannin ƙungiyar Gyara Kayanka daga ƙananan hukumomi daban-daban na jihar, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan hanyoyin da za a ƙara inganta haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin al’umma wajen magance ƙalubalen da ke addabar al’umma, musamman ta fuskar tsaro.

A cewar sa, tattaunawar na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na faɗaɗa haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin samar da mafita ga matsalolin da suka shafi zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Kwamishinan ya ƙara da cewa Gwamnatin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta kuduri aniyar tallafa wa duk wata ƙungiya ko tsari da ke bayar da gudunma wa wajen samar da tsaro, zaman lafiya da ci gaban al’umma.
“Mun yi imanin cewa dorewar tsaro da ci gaba ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, sai da cikakken haɗin kan al’umma da ƙungiyoyin da ke aiki domin cigaban jama’a,” in ji shi.
Waiya ya yabawa shugabanni da mambobin ƙungiyar Gyara Kayanka bisa gudunmawar da suke bayar wa, tare da tabbatar musu da cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida za ta ci gaba da mara musu baya da kuma duk wani tsari da ke inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al’ummar Jihar Kano.
