
Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da Manajan Tsarin Ruwan Yankin Thomas da Ghari bayan gano mummunar lalacewa da kuma sace-sacen kayan aiki a wurin aikin.
Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Dakta Hashim ya ce an ɗauki matakin ne bayan wata ziyarar gani da ido da ya kai wuraren ayyukan, inda ya bayyana halin da ya tarar a matsayin abin takaici da damuwa.
A cewarsa, cibiyoyin samar da ruwan da aka gina domin yi wa ƙananan hukumomi uku hidima sun kasance ba sa aiki tsawon shekaru, yayin da kusan dukkan wayoyin lantarki da ke haɗe da janareto da famfunan ruwa aka cire su.

Ya kuma bayyana cewa an sace kayan aikin wani sabon aikin samar da wutar lantarki da aka kammala watanni uku da suka gabata a Thomas, duk da cewa har yanzu ba a ƙaddamar da shi ba.
Bugu da ƙari, jami’an tsaron da aka ɗauka domin kare wurin aikin an same su suna noma a cikin harabar tashar ruwan maimakon gudanar da aikin da aka ɗauke su.
“Na bayar da umarnin dakatar da Manajan tsarin ruwan nan take har sai an kammala bincike. Idan binciken ya tabbatar da aikata laifi, gwamnati za ta ɗauki matakin shari’a yadda doka ta tanada,” in ji Kwamishinan.
Ya jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na da cikakken ƙudirin farfaɗo da harkokin samar da ruwa a jihar, yana mai cewa ana ci gaba da gyaran ayyukan ruwa na Chalawa da Tamburawa tare da shirye-shiryen dawo da dukkan tsare-tsaren ruwan yankuna aiki yadda ya kamata.
Dakta Hashim ya kuma yi kira ga al’umma da su taimaka wajen kare dukiyoyin gwamnati, yana mai cewa kadarorin jama’a mallakin kowa ne, don haka wajibi ne a kiyaye su domin amfanin al’umma baki ɗaya.Headline: Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Manajan Tsarin Ruwan Thomas da Ghari Kan Zargin Lalata Kayan Aiki
