
…Waɗannan mutane sun cancanci girmamawa, ba cin mutunci ba
Daga Munir Ibrahim Publisher
Yayin da ake ƙara kusantar babban zaɓen shekarar 2027, ana ci gaba da ganin sauye-sauyen siyasa da sabbin kawance a fagen siyasar Najeriya. Sai dai a lokaci guda, wani abin damuwa ya fara bayyana a tattaunawar jama’a, musamman a kafafen sada zumunta, inda muhawarar siyasa ke karkata daga tattauna manufofi zuwa cin mutunci da muzanta fitattun jagororin da suka kafa tarihi kuma suka taka muhimmiyar rawa wajen gina Arewa da Najeriya baki ɗaya.
A ‘yan watannin nan, kalamai masu zafi da nuna rashin girmamawa ga manyan mutane irin su Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da kuma Sir Abubakar Tafawa Balewa sun janyo damuwa a tsakanin al’ummar Arewa. Dukda cewa tarihin kowane shugaba na iya kasancewa abin nazari da muhawara ta ilimi, amma bai kamata a mayar da irin waɗannan manyan mutane abin zagi da tozarci ba.
A wurin mafi yawan ‘yan’arewa, waɗannan mutane alamu ne na sadaukarwa, hangen nesa da kuma gina tubalan ci gaba. Gudummawar da suka bayar a fannonin ilimi, shugabanci, bunƙasa yankuna da kuma gina ƙasa sun taimaka wajen samar da ginshiƙan da Najeriya ke ci gaba da amfana da su har zuwa yau. Saboda haka, duk wani saɓani game da tarihinsu ya kamata ya kasance cikin hujjoji da bincike mai zurfi, ba ta hanyar yaɗa ƙiyayya ko siyasantar da tarihi ba.
Haka kuma, akwai masu nuna damuwa kan yadda wasu ‘yan siyasa da jagororin siyasa suka kasa fitowa a fili su yi Allah-wadai da irin waɗannan kalamai daga wasu magoya bayansu. Ko da kuwa ba da gangan ake yi ba, yin shiru a irin wannan yanayi na iya haifar da zargin amincewa ko goyon baya ga irin waɗannan ɗabi’u.
Wannan muhawara ta kuma sake tayar da tattaunawa kan siyasar asali, tarihin ƙasa da kuma makomar Najeriya. Dukda bambance-bambancen ra’ayi da akidu na siyasa, babu wani dalili da zai sa a mayar da bambancin siyasa hanyar cin mutuncin waɗanda suka bayar da gudummawa ga ci gaban al’umma.
Ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya yana buƙatar a mayar da hankali kan muhawara mai ma’ana kan tsaro, ilimi, tattalin arziki, shugabanci da haɗin kan ƙasa, ba tare da tauye martabar waɗanda suka taka muhimmiyar rawa a tarihin ƙasar ba. Kowace ƙabila ko yanki na da jarumai da shugabannin da suka cancanci a girmama tarihinsu.
Yayin da ƙasar ke tunkarar wani sabon zangon zaɓe, ya zama wajibi ga ‘yan siyasa, ƙungiyoyin fararen hula, sarakuna, malamai da matasa su ƙarfafa al’adar tattaunawa cikin ladabi da mutunta juna. Girmama tarihi bai kamata ya zama abin zaɓi ba, kuma siyasa ba ta kamata ta zama hanyar gurɓata tarihin waɗanda suka yi wa al’umma hidima ba.
A ƙarshe, haɗin kan ƙasa da zaman lafiya na buƙatar haƙuri, fahimtar juna da mutunta mabambantan ra’ayoyi. Kodayake ‘yan Najeriya na iya saɓawa a siyasa, ya kamata su kasance masu haɗin kai wajen girmama sadaukarwa da gudummawar waɗanda suka taimaka wajen gina ƙasa da kuma shimfiɗa tubalan tarihin da muke alfahari da su a yau.
