
Daga Brown Pigeon Media
Jihar Kano ta shiga jimami bayan rasuwar tsohon Manajan Daraktan Radio Kano, Alhaji Adamu Ibrahim Getso, wanda ya rasu yana da shekaru 75 a duniya.
Marigayin, ɗan asalin garin Getso da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a Jihar Kano, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai da sadarwa a Arewacin Najeriya.
A tsawon shekarun aikinsa, Alhaji Adamu Getso ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin rediyo da wayar da kan jama’a, inda ya samu karɓuwa sosai a tsakanin masu sauraro da abokan aiki.
Ya taɓa zama Manajan Daraktan Abubakar Rimi Television (ARTV) a lokacin gwamnatin farko ta tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso. Haka kuma daga baya ya jagoranci Hukumar Radio Kano a wa’adin gwamnatin Kwankwaso na biyu.
Marigayin ya yi fice wajen gabatar da shirye-shiryen Hausa masu farin jini kamar Hukuma da Jama’a da kuma Aiki Sai Mai Shi, waɗanda suka mayar da hankali kan manufofin gwamnati, harkokin jama’a da ci gaban al’umma.
Masu sana’ar yaɗa labarai da dama sun bayyana shi a matsayin ƙwararren ɗan jarida kuma shugaba mai kishin ci gaban al’umma, wanda ya yi amfani da kafafen watsa labarai wajen ilimantar da jama’a da ƙarfafa hulɗa tsakanin gwamnati da al’umma.
Ya rasu ya bar mata, ‘ya’ya, jikoki da sauran ‘yan uwa.
Zu zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana musabbabin rasuwarsa ba, yayin da iyalansa ke sa ran sanar da shirye-shiryen jana’izarsa nan gaba kaɗan.
Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Amin.Brown Pigeon News.
