
Ƙungiyar tsofaffin masu taimakawa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta karrama Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, tare da naɗa shi a matsayin Mataimakin Uban Ƙungiyar, yayin da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ke matsayin Babban Uban Ƙungiyar.
An gudanar da bikin ne bayan wata ziyarar godiya da ƙungiyar ta kai wa kwamishinan, sakamakon amincewar Gwamnan Kano da biyan wasu haƙƙoƙin mambobinta da suka ce sun daɗe ba tare da karɓa ba tun daga gwamnatin da ta gabata.

Da yake jawabi, Shugaban ƙungiyar, Alhaji Gidado Ahmad Satatima, ya yabawa gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa abin da ya bayyana a matsayin adalci, kulawa da kuma cika alƙawarin da aka yi wa tsofaffin masu taimakawa gwamnati.
Ya ce ƙungiyar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin jihar, tare da alƙawarin ci gaba da mara mata baya wajen aiwatar da shirye shiryen ci gaban Kano.
Haka kuma, Satatima ya bayyana cewa ƙungiyar za ta yi aiki kafada da kafada domin ganin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu nasarar komawa kan kujerarsa a wa’adi na biyu, yana mai cewa haɗin kai da goyon bayan al’umma su ne ginshiƙan ci gaba da dorewar ayyukan raya jihar.
