
Ɓangaren marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankali kan harkokin gudanar da mulki wajen magance ƙalubalen tsaron da matsalolin tattalin arziki ko kuma ya sauka daga muƙaminsa, suna mai gargaɗin cewa Najeriya na fuskantar abin suka bayyana a matsayin mafi munin yanayin rashin tsaro da rashin tabbas a ɓangaren shari’a da koma-bayan dimokuraɗiyya daidai lokacin da ake fuskantar zaɓen 2027.
Yan majalisar sun kuma yi kira ga shugaban ƙasa da ya dakatar da harkokin siyasar neman sake zaɓensa ta hanyar mayar da martani don magance ƙalubalen tsaro da ke ƙaruwa da matsalolin tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.
Shugaban masara rinjaye na Majalisar, Fred Agbedi, ya yi wannan kiran ne a lokacin wani taron manema labarai da ‘yan majalisar adawa suka gudanar a Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Abuja ranar Laraba, inda suka zargi gwamnati da fifita siyasa fiye da ƙalubalen da bukatun gaggawa na ƙasa.
Kano first

Wannan kiran da ‘yan majalisar adawa suka yi na zuwa ne bayan ƙaruwar matsalolin tsaro a fadin ƙasar, ciki har da sace yara ƴan makaranta a jihohin Borno da Oyo da har yanzu suke hannun ‘yan bindiga; sace dalibai a Kogi da mutuwar tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe Mai Ritaya a maboyar masu garkuwa da mutane, da sauransu.
Al’ummomi a fadin jihohi masamman arewaci kamar Plateau da Kwara da Niger da Benue da Sokoto da Zamfara sun fuskanci hare-hare da kashe-kashe daga ‘yan bindiga wanda ya kai ga korar daruruwan mazauna.
A ranar Talata, shugabannin addin Musulmi da ɓangaren Katolika na Najeriya sun nuna damuwa kan yanayin tsaron ƙasar, inda suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa don dakile ci gaba da kashe-kashe, sace-sacen mutane da sauran ayyukan ɓata gari.
