
Daga Mohammed Babagana Abubakar
A daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da zama babban ƙalubale ga jihohin Arewacin Najeriya, Jihar Kano ta fito da wani sabon salo na magance matsalar ta hanyar gyaran hali, ƙarfafa matasa da haɗa al’umma cikin harkokin tsaro. Wannan tsari ne da ya sanya jihar ta zama abin koyi a yankin Arewa maso Yamma tare da jawo wa Gwamna Abba Kabir Yusuf takarar babbar lambar yabo ta ƙasa a fannin shugabancin tsaro.
Cibiyar Nazarin Tsaro da Dabarun Tsaro (Institute of Security and Strategic Studies) ta zaɓi Gwamna Abba Kabir Yusuf domin karɓar lambar yabo ta Award of Excellence in Security Governance bayan wani bincike da ta gudanar a jihohin Arewa maso Yamma bakwai. Binciken ya nuna cewa Kano ce ta fi nuna juriya wajen fuskantar ƙalubalen tsaro, aiwatar da manufofi masu inganci da kuma gaggawar martani ga barazanar tsaro.
Babban abin da ya ja hankalin masu tantancewar shi ne Shirin Safe Corridor, wanda gwamnatin Kano ta ƙaddamar domin gyarawa da sake mayar da matasa masu fama da shaye-shaye da munanan ɗabi’u cikin rayuwa mai amfani.
Kano first

Masana sun daɗe suna bayyana cewa talauci, rashin aikin yi, rashin ilimi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke tura matasa zuwa aikata laifuka. A maimakon jiran matsalar ta ta’azzara, gwamnatin Kano ta zaɓi magance tushen matsalar tun daga farko.
Shirin ya bai wa dubban matasa damar gyaran hali, samun ilimi da koyon sana’o’i domin su zama masu amfani ga kansu da al’umma. Fiye da matasa 3,000 ne suka nuna sha’awar shiga shirin, yayin da aka fara da gyaran hali ga matasa 1,000 a wani sansani na kwanaki 40 tare da haɗin gwiwar Hukumar NDLEA.
Baya ga wannan, gwamnatin ta ƙarfafa Rundunar Kano State Neighbourhood Watch Corps ta hanyar ɗaukar sama da matasa 2,000 aiki, ta horas da su tare da ba su kayan aiki da ofisoshi domin taimaka wa jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Haka kuma, an kafa runduna ta musamman domin yaƙi da masu ƙwacen waya da sauran laifukan tituna, lamarin da ya taimaka wajen rage irin waɗannan matsaloli musamman a cikin birnin Kano.
Wannan nasara ta nuna cewa tsaro mai ɗorewa ba ya samuwa ta hanyar amfani da ƙarfi kaɗai. Yana buƙatar saka hannun jari a cikin mutane, samar da dama ga matasa da kuma gina haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma.
Saboda haka, takarar Gwamna Abba Kabir Yusuf ta wannan babbar lambar yabo ba kawai yabo ga mutum ɗaya ba ce, illa yabo ne ga wata manufa ta shugabanci da ta mayar da rigakafin laifi, gyaran hali da ci gaban jama’a a matsayin ginshiƙan zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.
