
BROWN PIGEON
Gwamnatin Jihar Kano na nazarin shirin kafa kamfanin jirgin sama mallakar jihar Kano domin bunkasa tattalin arziki da sauƙaƙa zirga-zirga.
Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a , yayin da yake tattaunawa da alhazan Kano da ke Makka, a kasar Saudiyya.
Gwamnan ya ce, bisa la’akari da muhimmancin harkar jirgin sama a duniya, kamfanin jirgin sama na jiha zai taimaka wajen daukaka Kano, da kare muradun al’umma dana gwamnati, da kuma samar da sababbin hanyoyin samun kudin shiga.
Ya kara da cewa, kamfanin zai baiwa jihar kano sassauci wajen tsara zirga-zirga, da taimaka wa harkokin kasuwanci, ya kuma inganta hanyoyin zuwa sauran sassan Najeriya da kasashen waje.
Haka kuma a nan gaba kamfanin zai iya rike jigilar alhazai domin saukaka matsalar sufuri a yayin aikin Hajji da Umra.
Kano first

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatarwa alhazai cewa an yi shirye-shirye don dawo da su cikin sauki, inda jigilar zata fara a ranar 24 ga wannan wata.
Ya ce gwamnatinsa na ci gaba da neman sababbin dabaru na bunkasa ayyuka, da samar da ayyukan yi da karfafa tattalin arzikin jihar Kano.
Masana na ganin wannan shiri zai sanya Kano ta zama babbar cibiyar kasuwanci da zuba jari a fannin jirgin sama a Najeriya.
