
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya taya ‘yan Najeriya da mazauna Jigawa murna akan ranar Dimokuraɗiyya ta 2026, yana mai cewa 12 ga Yuni ranar tunawa ce akan sadaukarwar jarumai da suka yi gwagwarmaya domin adalci da ‘yancin zaɓe…
A cikin sakon sa, Gwamnan ya ce ranar wata dama ce ta nazarin tafiyar dimokuraɗiyya ta Najeriya da alhakin da ke kan shugabanni da jama’a wajen ƙarfafa cigaban bangarori.
Ya bayyana cewa dimokuraɗiyya ba zaɓe kaɗai ba ce, har da gina cibiyoyin da jama’a ke amincewa da su da, da bin doka da oda, da kare haƙin ɗan ƙasa, da tabbatar da gwamnati ta yi wa jama’a hidima.
Kano first

Gwamna Namadi ya ce ko da yake akwai ƙalubale, Najeriya ta samu cigaba ta hanyar tattaunawa da haƙuri.
A Jigawa kuwa, ya ce shirin sa na saka kudirori 12 a gaba” ya sa kimiyya wajen bunkasa ilimi, da lafiya, da noma, da ababen more rayuwa da tsaron jama’a
Ya yabawa sarakuna, da malamai, da jami’an tsaro da al’umma bisa ba da gudunmawa wajen zaman lafiya a jihar ta Jigawa.
Gwamnan ya kuma jaddada goyon bayansa ga shirin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da addu’ar samun zaman lafiya da wadata ga Jigawa da Najeriya baki ɗaya.
