
Rahotanni na cewa Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun fara daukar matakan aiwatar da tsare-tsaren hadin gwiwa domin rage talauci daya yiwa yankin katutu.
Daga cikin matakan gwamnonin sun dauki hanyar fadada shirye-shiryen kariyar zamantakewa da samar da sabbin hanyoyin samar da kudade a jihohi bakwai na yankin.
An gudanar da wannan shiri a Kano yayin wani babban taron tattaunawa na yini biyu daya gudana kan rage talauci ta hanyar inganta tsarin kariyar zamantakewa.
Kano first

Taron wanda dandalin Gwamnonin Arewa maso Yamma ta shirya tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya da tallafin Tarayyar Turai da UNICEF.
Da take jawabi yayin bude taron, babbar daraktar sakatariyar Dandalin Gwamnonin Arewa maso Yamma, Maryam Yahaya, ta ce tattaunawar muhimmin mataki ne na mayar da alkawuran yanki zuwa aikace-aikacen da za su inganta rayuwar miliyoyin jama’a.
Ta bayyana cewa duk da dimbin karfin tattalin arziki da albarkatun bil’adama da yankin ke da su, har yanzu Arewa maso Yamma na fama da manyan kalubale da suka hada da talauci, lafiya, rashin tsaro, illolin sauyin yanayi da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
