
Tsohon Kwamishinan Sufiri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi Dala, ya bayyana cewa babu wani ɗan takara daga kowace jam’iyyar siyasa da zai iya karawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen gwamnan jihar Kano mai zuwa, la’akari da dimbin ayyukan ci gaba da gwamnatin sa ta aiwatar da kuma irin goyon bayan da yake samu daga al’ummar jihar.
Alhaji Ibrahim Ali Namadi Dala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a birnin Kano.
Ya ce a cikin shekaru uku kacal da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi yana jagorantar jihar Kano, ya aiwatar da ayyukan raya ƙasa da walwalar al’umma da suka shafi ilimi, lafiya, samar da ababen more rayuwa da kuma bunƙasa tattalin arziki, wanda yace hakan ce ta sa al’umma ke ci gaba da yaba wa gwamnatinsa.
Tsohon kwamishinan ya ƙara da cewa irin nasarorin da gwamnatin ta samu ne suka sanya jama’a da dama ke kallon Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin zaɓin da ya dace domin ci gaba da jagorantar jihar Kano.
Dangane da siyasar Ƙaramar Hukumar Dala, Alhaji Namadi Dala ya bayyana yankin a matsayin ɗaya daga cikin manyan sansanonin APC, yana mai nuna tabbacin cewa jam’iyyar za ta samu gagarumar nasara a zaɓe mai zuwa.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Kano da su yi nazari mai zurfi kan ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar, tare da goyon bayan ‘yan takarar APC a dukkan matakai domin tabbatar da dorewar ci gaba da ayyukan alheri da ake aiwatarwa a jihar.
A cewarsa, ci gaban da Kano ke samu a halin yanzu na buƙatar haɗin kan al’umma da kuma zaɓen shugabannin da za su ci gaba da tafiyar da manufofin ci gaba da gwamnati ta fara aiwatarwa.
