
Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang, ya ce gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawar sulhu da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka ba, yana mai cewa za’a ci gaba da daukar matakan tsaro domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Mutfwang ya bayyana haka a taron ranar dimokuraɗiyya da aka gudanar a Jos ranar Juma’a.
Mutfwang ya ce tattaunawa da ‘yan ta’adda ba za ta zama mafita ba, yayinda jami’an tsaro za su ci gaba da gudanar da aiyukan da suka dace kan masu hannu a hare-haren ta’addanci.
Kano first

Ya ce haɗin gwiwar da gwamnatin jihar ke yi da jami’an tsaro da shugabannin al’umma ya fara haifar da sakamako mai kyau, inda aka kama wasu da ake zargi da hannu a hare-haren da suka faru a sassan jihar.
Ya ci gaba da cewa binciken da ake yi na taimakawa wajen gano manyan hanyoyin sadarwa da masu aikata laifuka ke amfani da su, yayin da gwamnati ke ci gaba da tallafawa jami’an tsaro da kayan aiki da bayanan sirri.
Mutfwang ya yabawa Shugaba Bola Ahmad Tinubu kan abin da ya kira da cikakken goyon baya ga jami’an tsaro wajen yaƙi da tabarbarewar tsaro a ƙasar.
