
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta na farfaɗo da sake fasalta Triumph Newspapers domin ta dawo da martabarta a matsayin babbar kafar yaɗa labarai a Arewacin Najeriya.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, tare da Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Sa’ad Amin, sun kai ziyara hukumar gudanarwar Triumph Newspapers domin duba halin da kamfanin ke ciki da kuma gano matsalolin da ke kawo cikas ga ayyukansa.
Mukaddashin Manajan Daraktan kamfanin, Muhammad Hamisu Abdullahi, ya bayyana cewa Triumph na fuskantar ƙalubale da suka haɗa da rashin wadataccen wutar lantarki, ƙarancin kwamfutoci da sauran kayan aikin zamani.
Ya roƙi Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta taimaka wajen magance matsalolin domin Triumph ta koma kan turbar da ta saba a tarihi.
A nasa jawabin, Kwamishina Waiya ya ce gwamnati ta fahimci muhimmancin Triumph Newspapers, yana mai bayyana ta a matsayin cibiya da ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa aikin jarida da horar da ƙwararrun ‘yan jarida.
Waiya ya bayyana cewa ya riga ya gabatar da batun farfaɗo da Triumph a gaban Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano, yana mai cewa ana buƙatar mafita mai ɗorewa.
Shi ma Hon. Sa’ad Amin ya tabbatar da cewa Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar zai yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen tallafa wa ƙoƙarin farfaɗo da zamanantar da Triumph Newspapers.
Ya jaddada cewa farfaɗo da kamfanin na buƙatar haɗin gwiwar gwamnati, majalisa, tsofaffin ma’aikata, ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki.
