
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya karɓi bakuncin shugabannin Ƙungiyar Daliban ’Yan Asalin Jihar Kano da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Kwamared Abdulrahman Bala.
A yayin ziyarar, shugabannin ƙungiyar sun tabbatar wa Kwamishinan cewa za su ci gaba da bai wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, cikakken goyon baya tare da mara masa baya a babban zaɓen shekarar 2027.
Haka kuma, daliban sun roƙi Kwamishinan da ya shiga gaba wajen isar da buƙatunsu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman bukatun da suka shafi harkar ilimi, tallafi da sauran abubuwan da za su taimaka wajen inganta rayuwar ɗaliban ’yan asalin Jihar Kano.
A nasa ɓangaren, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya tabbatar musu da cewa zai gabatar da buƙatunsu ga Mai Girma Gwamna, musamman waɗanda suka shafi ilimi da sauran buƙatun dalibai.
Kwamishinan ya kuma gode wa shugabannin ƙungiyar bisa ziyarar da suka kai masa, tare da yi musu fatan alheri da samun ci gaba mai ɗorewa.
