
Daga Mutawakkilu Ibrahim Idris
Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga limaman masallatan Juma’a a fadin jihar da su yi amfani da hudubar Juma’a wajen wayar da kan jama’a kan muhimmanci da kuma alfanun shirin auren gata da gwamnatin jihar ke gudanarwa.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya yi wannan kiran yayin da yake karbar bakuncin kungiyar matasan limaman masallatan Juma’a ta Kano a wani taro da aka gudanar a Kano.
Waiya ya jaddada muhimmiyar rawar da limamai da malaman addinin Musulunci ke takawa wajen ilmantar da al’umma, karfafa zaman lafiya da hadin kai, da kuma dakile yada bayanan karya da ka iya haifar da rashin fahimta a tsakanin jama’a.
Kwamishinan ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu hotunan wasu tsofaffin mutane ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ake ikirarin cewa suna daga cikin wadanda aka aurar a karkashin shirin auren gata na Gwamnatin Jihar Kano.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin tsofaffin mutanen da aka nuna a cikin hotunan tsofaffin jami’an Hukumar Hisbah ne da suka yi ritaya daga aiki, yana mai cewa kasancewarsu a wajen taron bai kamata a fassara shi da cewa sun kasance cikin wadanda suka amfana da shirin auren gata ba.
Saboda haka, Waiya ya bukaci limamai da sauran shugabannin addini da su taimaka wajen wayar da kan jama’a kan gaskiyar abin da ya shafi shirin, tare da yin gargadi kan yada jita-jita, labaran karya da bayanan da za su iya batar da jama’a, musamman a kafafen sada zumunta.
Ya ce shugabannin addini suna da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa jama’a sun samu sahihan bayanai tare da fahimtar manufofin shirye-shiryen gwamnati da ake aiwatarwa domin tallafa wa iyalai da karfafa zamantakewar al’umma a jihar.
Tun da farko, shugaban kungiyar, Imam Gwani Sani Tilo, ya yaba wa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wasu shirye-shiryen da take aiwatarwa da suka shafi inganta rayuwar al’ummar Kano, musamman shirye-shiryen da suka shafi harkokin addinin Musulunci da jin dadin al’ummar Musulmi.
Imam Tilo ya kuma bayyana dalilan da suka sa kungiyar ta sauya daga tsohuwar turbar siyasarta tare da mara wa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Gwamna Abba Kabir Yusuf baya.
Ya ce kungiyar ta kasance cikin harkar siyasar da ta taimaka wajen samar da gwamnatin da ake da ita a Kano, don haka ta yanke shawarar ci gaba da mara wa gwamnatin baya wajen kokarinta na samar da ci gaba ga al’ummar jihar.
Shi ma da yake nasa jawabin, daya daga cikin limaman, Imam Zubairu Al-Muhammadi, ya tabbatar wa Kwamishinan cewa kungiyar za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da kokarin ganin ya sake samun nasara a zaben gwamnan jihar na shekarar 2027.
Ya danganta goyon bayansu ga abin da ya bayyana a matsayin kyakkyawan halin Gwamnan, jajircewarsa wajen gudanar da aikin gwamnati da kuma shirye-shiryen raya kasa da yake aiwatarwa domin inganta rayuwar al’ummar Kano.
A karshen taron, mahalarta sun jaddada bukatar kara hadin gwiwa tsakanin shugabannin addini, gwamnati da sauran al’umma wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, yada sahihan bayanai cikin kishin kasa da kuma samar da ci gaba mai dorewa a Jihar Kano.
