
By Mutawakkilu Ibrahim Idris
Mai Girma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da bai wa fannin yaɗa labarai muhimmanci domin tabbatar da isar da sahihan bayanai ga al’umma.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da ya halarci taron bita na musamman na kwanaki biyar da Gidan Rediyon Kano ya shirya domin ƙara wa juna sani da bunƙasa ƙwarewar ma’aikata da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai.
Taron, wanda Shugaban Gidan Rediyon Kano, Adamu Rano, ke jagoranta, na da nufin inganta aikin yaɗa labarai, musayar ƙwarewa da kuma samar da sabbin dabarun da za su dace da sauye-sauyen zamani.
A jawabinsa, Waiya ya ce irin waɗannan shirye-shiryen horaswa suna ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata tare da inganta ayyukan kafafen yaɗa labarai.
Ya kuma yaba da shugabancin Gidan Rediyon Kano kan shirya taron, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa fannin domin bunƙasa aikin jarida da sadarwa.
– Brown Pigeon Media
