
Fitaccen mawakin siyasa a Arewacin Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Buhari Kosan Waka, ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya. Rahotanni sun tabbatar da rasuwarsa a yau, lamarin da ya jefa masoya, abokai da al’ummar siyasa cikin jimami.
Marigayin ya yi suna wajen rera wakokin siyasa da na fadakarwa, inda ya shafe shekaru yana amfani da basirarsa wajen isar da sakonni kan al’amuran siyasa da zamantakewa. Wakokinsa sun yi tasiri sosai a fadin Arewacin Najeriya, musamman a lokutan yakin neman zabe.
Bayan samun labarin rasuwarsa, mutane da dama sun fara mika sakonnin ta’aziyya tare da bayyana alhininsu, suna yabawa gudunmawar da ya bayar ga harkar waka da siyasa.
Ana sa ran iyalansa da na kusa da shi za su sanar da cikakken bayani kan shirye-shiryen jana’izarsa.
Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Amin.
